Iklan Billboard 970x250

Saurayin Ummi Rahab Ya Tona Asirin Adam A Zango

Featured Post

New Episode: Island Season 1 Episode 8

Johan overcomes his despair after Chan-hee's death. Mi-ho, who is in pain and blaming herself, vows not to lose anyone else who is precious. From then, she begins receiving intense training... >>> Watch and Downl…

Saurayin Ummi Rahab Ya Tona Asirin Adam A Zango

Yanzu yanzu muka samu wani sabon faifan video ya bayyana akan rikicin Adam A Zango da Ummi Rahab.

Saurayin yace da bayyi niyyar magana ba akan wannan rigima, amma sai yaga cewa akwai lauje cikin nadi a cikin lamarin.

Dalilin hakane ma yasa shi wannan saurayi ya yanke shawarar yin faifan bidiyon don bayyana ma mutane abunda ke faruwa.

Duba da irin yadda mutane keta yada karya da gaskiya akan wannan chakwakiya tsakanin Ummi Rahab da Adam A Zango.

Inda zakaga wasu na zagin Ummi Rahab, wasu kuma na zagin Adam A Zango.

Ummi Rahab dai tayi shiru kuma taki tayi hira da shafin Hausa na BBC akan abinda yake faruwa tsakaninta da Adam A Zango.

Amma shi Adam A Zango yayi magana inda ya bayyana cewa Ummi Rahab tamkar ‘ya take a gurinsa duk da bashi ya haifata ba.

Amma kuma sai gashi reshe ya juye da mujiya akan rayuwar Ummi Rahab da kuma Adam A Zango.

Adam A Zango yace kowane lokaci yana kokarin da ganin ya faranta ran jaruma Ummi Rahab.

Amma kash! sai gashi mahassada sun shiga tsakanin su inda hakan takaisu ga rabuwa.

Daga karshe dai Adam A Zango ya bayyanawa BBC Hausa cewa ya zurawa Ummi Rahab ido tayi abinda take so.

Wata rana gaskiya zatayi halinta kuma zata gane cewa shi masoyinta ne na gaskiya.

The post Saurayin Ummi Rahab Ya Tona Asirin Adam A Zango appeared first on Blogloaded.



from KuryaNg.Com https://ift.tt/3DejdWs August 24, 2021 at 03:56AM https://kuryang.com
Baca Juga
SHARE
Subscribe to get free updates

Related Posts

Post a Comment

Iklan Tengah Post